Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Yi wa Ma'aikata Karin Albashi – Tinubu


Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Tinubu ya kuma jinjinawa kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kansu da suka riga suka yi karin albashi.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi karin albashi a nan gaba kadan.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa ‘yan kasar da yammacin Litinin.

“Muna aiki tare da kungiyoyin kwadago domin samar da sabon albashi mafi karanci.

“Da zarar mun kammala tattaunawa, za mu sama masa gurbi a kasafin kudinmu domin a fara aiwatar da shi.” Tinubu ya ce a jawabin nasa mai tsawon minti 21.

Kazalika ya nemi ‘yan Najeriya da su kara hakuri, yana mai cewa gwamnatinsa ta daura damara wajen ganin ta kyautata rayuwar al’umar kasar.

Tinubu ya kuma jinjinawa kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kansu da suka riga suka yi karin albashi.

Shugaban na Najeriya ya kuma zayyana wasu shirye-shirye da su gabatar wadanda za su karfafa fannin masana'antun kasar yana mai cewa tuni sun dauki matakai wajen fitar da abinci don wadatar al'umar kasar.

Gabanin jawabin, ‘yan Najeriya da dama sun kasa kunne su ji abin da shugaban zai fada a jawabin nasa, tun bayan da fadarsa ta fitar da sanarwar cewa zai yi jawabin.

Tun dai bayan da aka cire tallafin mai a watan Mayu, ‘yan Najeriya suke ta korafi kan yadda rayuwa ta yi tsada.

Farashin man fetur ya yi tashin goron-zabi bayan da Tinubu ya sanar da cire tallafin man bayan da aka rantsar da shi, lamarin da ya shafi fannonin rayuwar al’uma da dama.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG