Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok Da Suka Kubuta Za Ta Yi Aure A Amurka


Bishara da angonta James
Bishara da angonta James

Joy Bishara, daya daga cikin ‘yan mata dalibai da suka kubuta bayan da mayakan Boko Haram suka sace su a garin Chibok za ta yi aure a Amurka.

Bishara ce ta wallafa labarin a shafinta na Facebook a ranar Talata. Ta bayyana sunan rabin ran nata a matsayin James.

Lokacin da James ya nemi amincewa Bishara don su yi aure (Facebook/Joy Bishara)
Lokacin da James ya nemi amincewa Bishara don su yi aure (Facebook/Joy Bishara)

“Yanzun nan na mika wuya ga kauna, raha kuma babban aboki.” Bishara mai shekaru 27 ta wallafa a shafinta hade da hotunan saurayin nata da suka yi baiko tare.

“Ina mai matukar farin cikin fara wannan tafiya da abin kaunata …. Mata da miji na nan tafe.” Bishara ta kara da cewa.

Bishara da James (Facebook/Joy Bishara)
Bishara da James (Facebook/Joy Bishara)

A watan Afrilun 2014, mayakan Boko Haram suka far wa makarantar sakandaren garin Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, suka sace dalibai mata sama da 270.

Sai dai 57, cikinsu, har da Bishara, sun arce bayan da suka dira daga motocin da aka kwashe su.

Wannan lamari ya ja hankalin duniya, ya kuma ba wasu daga cikin wadannan ‘yan mata da suka kubuta damar yin kaura zuwa Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG