Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen yankin Yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO, ta Allah yi wadai da yunkurin juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ke jagorantar kungiyar, ya ce ECOWAS ba za ta taba lamuntar juyin mulki a kasar ta Nijar ba wacce ke makwabtaka da Najeriya.
Cikin wata sanarwa da ECOWAS ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Laraba, kungiyar ta yi kira ga dakarun da ke da hannu a yunkurin juyin mulki da su hanzarta sakin shugaban kasar wanda ta ce an zabe shi ne bisa tsarin dimokradiyya.
“Ya kamata dukkan masu ruwa da tsaki a Jamhuriyar Nijar su fahimci cewa, shugabancin kungiyar ECOWAS da sauran masu muradun tsarin mulkin dimokradiyya a sassan duniya, ba za su lamunci duk wani abu da zai gurgunta tsarin mulkin dimokradiyya da aka kafa na zababbiyar gwamnati a kasar ba.” Tinubu ya ce cikin wata sanarwa da ya fitar ta daban.
Ya kara da cewa, “a matsayina na shugaban kungiyar ECOWAS, ina mai nuna cikakken goyon bayan Najeriya ga zababbar gwamnatin Nijar ina kuma mai bayyana matsayar kungiyarmu cewa, ba za mu taba nuna gazawa ba wajen kare tsarin da doka ta bamu ba."
Kungiyar ta ECOWAS har ila yau ta yi gargadin cewa, za ta dora alhakin duk wani abu da ya faru da Shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa ko sauran mukarraban gwamnati akan wadanda ke da hannu a yunkurin juyin mulkin.
Da sanyin safiyar yau Laraba ne bayanai suka nuna cewa wasu dakaru da ke tsaron fadar shugaban kasar ta Nijar da ke birnin Yamai, sun rufe dukkan hanyoyin shiga fadar tare da tsare Shugaba Bazoum.
Lokaci na karshe da aka yi yunkurin juyin mulki a kasar ta Nijar shi ne a watan Maris din 2021, kwanaki biyu gabanin shugaba Mohamad Bazoum ya karbi mulki.
Saurari karin rahoto daga Umar Farouk Musa:
Dandalin Mu Tattauna