Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Zai Yi Wa ‘Yan Najeriya Jawabi Yau Litinin

Chairperson of Economic Community of West African States (ECOWAS) and President of Nigeria, Bola Ahmed Tinubu, reacts while addressing the ECOWAS head of states and government in Abuja on July 30, 2023

Sai dai sanarwar ba ta ambaci takamaiman dalilin da ya sa shugaban wanda ya karbi mulki  a watan Mayu zai yi jawabin ba.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi yau Litinin.

Wata sanarwa da kakakinsa Dele Alake ya sanyawa hannu ta ce jawabin na Tinubu zai zo ne da misalin karfe bakwai na dare agogon Najeriya.

Sai dai sanarwar ba ta ambaci takamaiman dalilin da ya sa shugaban wanda ya karbi mulki a watan Mayu zai yi jawabin ba.

‘Yan Najeriya dai na fama da matsalolin da suka shafi tsaro da kuma tsadar rayuwa, wani abu da masana ke cewa su ke ci wa ‘yan kasar tuwo a kwarya.

Jim kadan bayan karbar mulki, Tinubu ya soke shirin na tallafin mai, lamarin da ya cilla farashin man fetur zuwa sama.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG