Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata DSS Ta Gayyaci Davido – MURIC


Davido
Davido

Tuni dai Davido ya cire bidiyon a shafukansa na sada zumunta bayan da aka yi ta sukar shi a dandalin yanar gizo.

Kungiyar da ke kare hakkin Musulmi ta MURIC a Najeriya, ta yi kira ga hukumar tsaron farin kaya ta DSS da ta gayyaci mawaki David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido saboda wani bidiyo da ya wallafa, wanda al’umar Musulmin kasar ta yi Allah wadai da shi.

Babban Darektan kungiyar ta MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A karshen makon da ya gabata Davido ya wallafa bidiyon Logos Olori, wani sabon matashin mawaki, wanda ya nuna wasu mutane sanye da jallibiya suna sallah inda daga baya kuma suka bige da rawa a inda suka yi sallar, lamarin da Musulmi suka bayyana a matsayin batanci ga addininsu.

A bidiyon har ila yau, an ga Olori a cikin wakar tasa mai suna “Jaye Lo” wacce Davido ya wallafa, ya zauna a saman wani masallaci yana raye-raye.

“Muna masu jan hankalin jami’an DSS, da su gayyaci mutanen biyu (Davido da Olori) don amsa tambayoyi kan dalilinsu na yin wannan bidiyo da zai iya ta da fitina a Najeriya.” Farfesa Akintola ya ce.

MURIC har ila yau, ta yi kira ga hukumar da ke kula da kafafen watsa labarai ta NBC da ta tace fina-finai (NFVCB), da “su haramta wannan bidiyo na wakar ‘Jaye Lo’ da Logos Olori ya yi.”

Tuni dai Davido ya cire bidiyon a shafukansa na sada zumunta bayan da aka yi ta sukar shi a kafafen sada zumunta.

Daga cikin fitattun mutanen da suka soki Davido, akwai jarumin Kannywood Ali Nuhu da tsohon mai bai wa tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shawara kan sha’anin kafafen sada zumunta Bashir Ahmad.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG