Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa hukumomin Najeriya sun katse wutar lantarkin da suke samar wa makwabaciyarsu Jamhuriyar Nijar.
Matakin na zuwa ne kwanaki bayan da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS/CEDEAO ta kakaba takunkumi kan kasar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi.
A ranar 26 ga watan Yuli, dakarun da ke tsaron fadar shugaban kasar ta Nijar suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.
“Tun jiya (Talata) Najeriya ta katse babbar hanyar layin da take ba Nijar wuta.” Wata majiya a kamfanin wutar lantarki na Nigelec ta fadawa AFP.
Kashi 70 cikin 100 na wutar da Nijar take saya daga Najeriya ne wacce ake tatso ta daga madatsar ruwa ta Kainji Dam.
Baya ga matsalar ta wutar lantarki, a bankuna ma an fara fuskantar tsaikon hada-hada inda masu kokarin cire kudade ke cincirindo a wani lokaci da aka fara fuskantar karancin masu ajiya saboda fargabar abin da ka iya zuwa ya komo.
Dandalin Mu Tattauna