Al’umar garin Kajuru Station sun tabattar wa Muryar Amurka dawowan mutane uku cikin 87 da ‘yan bindiga suka sace a ranar Lahadin da ta gabata.
Malama Khadija AbdulRa'uf Kuriga, daya daga cikin iyaye matan da ke cikin dimuwar kwashe daliban, ta nuna matukar damuwarta kan rashin sanin halin da sauran daliban ke ciki.
Rundunar yan-sandan jihar Kaduna ta tabbatar da sace daliban wata makaranta da ke yankin Kurigan a karamar hukumar Chikun, to sai dai ta ce ba ta tantance adadin daliban da aka sace ba yayin da al’ummar garin ke cewa daliban sun kai dari biyu.
Ganin yadda matsalolin tsaro su ka ki ci, su ka ki cin yewa ya sa gwamnatin Najeriya shan alwashin sauya salo ta hanyar amfani da kimiyyar zamani wajen fuskantar 'yan-bindiga da sauran masu laifuffuka don magance matsar tsaro baki daya.
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kashe Boderi Isyaku kasurgumin dan-fashin dajin nan da ya addabi jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara Naija da Abuja, tare da wasu manyan 'yan-bindigan dake tare da shi.
Duk da ganin zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa da wasu 'yan-Najeriya su ka fara, wasu shugabanni sun ce duk wani bore ba zai taimaki Najeriya ba.
Shugabanni a gundumar Kufanan karamar hukumar Kajurun da 'yan bindiga su ka kai hari, sun ce kone mutane da rumbunan abinci da aka yi babbar barazana ce ga al-umar garin Gindin Dutse Makyalin.
Al’umomin garuruwan yammacin Zaria sun koka kan hauhawar hare-haren 'yan-bindiga a yankin da su ka ce kullum sai an kashe musu mutane kuma a sace wasu don karbar kudin fansa.
Ganin yadda talakawa su ka fara zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa a wasu yankunan Najeriya ya sa Majalissar Limamai da Malamai ta jihar Kaduna jawo hankalin gwamnati don kada a bar lamarin ya kazance.
Gobarar, da ta tashi cikin dare a kasuwar Panteka tsohowa dake cikin garin Kaduna, ta lakume rumfunan masu sayar da katako sama da hamsin kafin zuwan 'yan kwana-kwana wadanda su ka kashe ta.
Sama da kwanaki arba'in da harin jirgin sojan da su ka ce kuskure ne a garin Tudun Biri, wasu al’ummar yankin sun ce har yanzu gwamnati ba ta cika musu alkawurran da ta dauka ba.
Dukkan ‘yan majalisar dattawa 109 na Najeriya sun ce sun sadaukar da albashin su na wannan watan Disamba gaba daya ga iyalan wadanda su ka rasu sanadiyyar harin jirgin saman soji a garin Tudun Biri na jihar Kaduna.
Ganin yadda adadin wadanda su ka rasu sanadiyyar harin bam na jirgin sojan Najeriya yake karuwa bayan rasuwar wasu masu jinya, hadakar kungiyoyin matasa a Arewacin Najeriya sun gudanar da zanga-zangar nuna damuwa kan abin da ya faru a garin Tudun Biri na Karamar Hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Ana kara samun karuwar mutanen da su ka rasu biyo bayan harin kuskure na jirgin sojan kasan Najeriya kan masu taron Mauludi a garin Tudun Biri na Karamar hukumar Igabin jihar Kaduna, yayin da 'yan-uwa da iyalan wadanda abin ya shafa suka ce wasu masu jinya a asibiti sun kara rasuwa a ranar Talata.
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da harin jirgin sama mara matuki da ya hallaka wasu masu taron Mauludi a garin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi, sai dai ta ce kuskure aka samu kuma har yanzu ba a tantance adadin wadanda su ka rasu ba.
Domin Kari