Kwana daya da sace dalibai 287 a garin Kuriga da ke Karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, daya daga cikin daliban ya kubuta.
Sai dai iyayen dalibin sun nuna damuwa da irin halin da yake ciki yayin da iyaye mata ke ta kuka kan rashin sanin halin da sauran daliban ke ciki.
A ranar Alhamis ‘yan bindiga suka sace dalibai 187 a bangaren sakandire da kuma 125 a bangaren firamare a garin Kuriga.
Tun da farko dalibai 25 sun samu sun gudo sai kuma a ranar Juma'a wani dalibin ya gudo cikin wani irin mummunan hali abin da ya kara ta da hankalin iyayen yaran.
Malama Khadija AbdulRa'uf Kuriga daya daga cikin iyaye matan da ke cikin dimuwar kwashe daliban, ta nuna matukar damuwarta kan rashin sanin halin da sauran daliban ke ciki.
Malam Sani Abdullahi na cikin malaman bangaren sakandiren da su ka tsira da ya ce 'yan-bindigan sun kashe dan-sintiri daya.
Tun a yammacin jiya Alhamis din da aka sace wadannan dalibai, Gwamna Uba Sani na jihar ta Kaduna ya ziyarci garin Kuriga.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu wani labari daga bangaren 'yan-bindigan da suka afkawa wannan makaranta.
Sai dai rundunar ‘yan-sandan jihar Kaduna ta ce ta riga ta baza jami'anta don ceto wadannan dalibai.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara na Muryar Amurka daga Kaduna a Najeriya:
Dandalin Mu Tattauna