A yayin da takaddama kan sanadin mutuwar dalibin Makarantar Al-Azhar da ke Zariya ta barke tsakanin Makarantar da kuma iyayen dalibin, rundunar 'yan-sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kama wasu mahukuntan Makarantar kuma ta ce bincike ya fara nisa.
Hauhawar hare-haren 'yan-bindiga a wuraren ibada ya sa kungiyar kiristoci ta kasa CAN, jawo hankalin rundunar 'yan-sandan jihar Kaduna kan adadin limamanta da 'yan-bindiga suka kashe cikin shekaru hudu.
Wasu daga cikin likitocin da suka kware a wannan fanni sun ce rashin fahimtar tasirin motsa jiki don kula da gabbai, yana matukar nakasa rayuwar mutane da dama a Najeriya.
Ganin yadda 'yan-bindiga ke neman sauya salo ta hanyar kai hare-hare wuraren ibada ya sa rundunar 'Yan-sandan jahar Kaduna kafa wani Kwamitin binciko musabbabin sabon salon harin don dakile shi.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da harin da wasu mahara dauke makamai a kan babura suka kai a gundumar Saya-Saya da ke karamar hukumar Ikara ta Jihar Kaduna, inda su ka kashe mutane a cikin masallaci a daren Juma'a.
Duk da sanar da samar da tallafin kudi da kayan abunci da gwamnatin tarayya ta yi don rage radadin kuncin rayuwa a Najeriya, Majalisar Malaman addinin Musulunci ta kasa ta ce tallafin ba zai yi wani tasiri ba.
Domin Kari