Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu ‘Yan Bindiga Na Kai Sabbin Hare-hare A Garuruwan Yammacin Zaria


Yan bindiga
Yan bindiga

Al’umomin garuruwan yammacin Zaria sun koka kan hauhawar hare-haren 'yan-bindiga a yankin da su ka ce kullum sai an kashe musu mutane kuma a sace wasu don karbar kudin fansa. 

KADUNA, NIGERIA - Al’umomi sun ce kullun sai sun bizine gawar mutanen da 'yan-bindiga kan kashe, banda maganar miliyoyin kudin fansa.

Al’umomin garuruwan yammacin Zaria dai sun ce yanzu rayukan mutanensu bai zama komai ba gurin 'yan-bindiga saboda yadda kusan kullum sai an kaiwa garuruwan hari.

Alhaji Dayyabu Kerawa wanda ya yi magana da yawun al’umomin yankin ya ce gaskiya turi ta kai bango.

Kafin yanzu dai an sami saukin hare-haren 'yan-bindiga a wasu yankunan na jihar Kaduna, sai dai dawowar hare-haren yasa masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai-ritaya ke cewa akwai abubuwan lura masamman ganin yadda hare-haren ke ta kara hauhawa a wasu yankunan jihar Kaduna.

Manjo Shinko ya ce akwai yuwuwar matakan da gwamnatocin Katsina, Zamfara da Sokoto su ka dauka ne ya hana 'yan-bindigan sukuni shi yasa suka dawo cikin Kaduna.

Kokarin jin tabakin jami'an tsaro dai ya ci tura saboda Muryar Amurka ta tura sako amma babu amsa har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Ko da yake gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya taba shaida mana matakan da gwamnati ke dauka, inda ya ce gwamnati ta hada kai da sarakuna da dakatai da masu unguwanni don tattara bayanan sirri sannan kuma gwamnatin tarayya za ta karowa jihar Kaduna jami'an sojoji.

Hare-haren 'yan-bindiga a wadan nan yankuna dai sun zo a dai-dai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa saboda kuma mutane dayawa a yankin ba su yi noma ba saboda matsalar tsaro sannan sayen abinci kuma ya gagara saboda tsada.

A saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara.

Har Yanzu ‘Yan Bindiga Na Kai Sabbin Hare-hare A Garuruwan Yammacin Zaria
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG