KADUNA, NIGERIA - Ministan tsaro a Najeriya, Malam Mohammad Badaru Abubakar wanda ya halarci taron bita ga malaman addinin Musulunci a garin Kaduna yau Talata ya ce nasara kan yaki da 'yan-sari-ka-noke na da matukar wuya.
Maganar matsalar tsaro da tsadar rayuwa dai sune manyan batutuwan da majalissar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya ta jawo hankalin kenan a wajen wannan taro, shi yasa ministan tsaron Najeriya Malam Mohammad Badaru Abubakar ya bayyana matakan da gwamnatin tarayya ke dauka don murkushe matsalar baki daya.
Ya ce yanzu da zaran 'yan-bindiga sun fito kafin su gama kai hari su koma daji jami'an tsaro sun gama da su ta hanyar gano inda su ke da kuma daukar matakin tarwatsasu.
To shin ko gwamnatin Najeriya za ta iya amfani da kimiyyar zamani don murkushe matsalar tsaro kamar yadda wasu jami'an ta su ka dinga ikirari a baya, wannan ce tambayar da Muryar Amurka ta yi wa masanin harkokin tsaro Manjo Yahaya Shinko mai-ritaya wanda ya ce idan har da gaske gwamnatin tarayya za ta yi amfani da kimiyyar zamanin abu ne mai yiwuwa sai dai kuma ya ce gwamnatin ta dade ta na makamantan wadannan alkawura ba tare da an gani a kasa ba.
Kafin maganar amfani da kimiyyar zamani, gwamnatin tarayya ta sha alwashin kirkiro 'yan-sandan jihohi don tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, sai dai kuma babban sakataren majalissar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya, Malam Nafi'u Baba Ahmed ya ce dole gwamnati ta taka a hankali.
Baba Ahmed ya ce gwamnoni za su iya amfani da 'yan-sandan jihohi wajen musgunawa 'yan-adawa da kuma karya ka'idojin aikin tsaron da ka iya zama matsala ga kasa.
Tuni dai ganin jan-kafar da ake ta samu kan kirkiro rundunar 'yan-sandan jihohi ya sa wasu yankuna da kuma daidaikun jihohin kirkiro rundunonin da ke aikin agazawa tsaro, sai dai duk da haka ba a daina samun matsalolin tsaron a wadannan jihohi da kuma yankuna ba.
Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara:
Dandalin Mu Tattauna