Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Da Ake Zaton Sun Kai 200 A Jihar Kaduna


Wasu ‘Yan bindiga
Wasu ‘Yan bindiga

Rundunar yan-sandan jihar Kaduna ta tabbatar da sace daliban wata makaranta da ke yankin Kurigan a karamar hukumar Chikun, to sai dai ta ce ba ta tantance adadin daliban da aka sace ba yayin da al’ummar garin ke cewa daliban sun kai dari biyu. 

KADUNA, NIGERIA - Da safiyar yau Alhamis ne dai 'yan-bindiga su ka yiwa makarantar Firamare da ake kira LEA Primary School Kuriga 1 Kawanya, inda su ka kora daliban makarantar 'yan tsakanin shekaru 7 zuwa 15 da daya daga cikin malaman makarantar zuwa daji.

Malam Aminu Jibrin Gwadabe Kuriga haifaffen garin Kuriga ne kuma ya yi wa Muryar Amurka karin bayanin bayan da ya tabbatar da aukuwar lamari da ya faru.

Tuni dai rundunar ‘yan-sandan jihar Kaduna ta tura jami'an tsaro yankin don bin 'yan-bindigan cikin daji, inji mai magana da yawun rundunar, ASP Mansur Ibrahim.

Wannan dai ba shine karon farko da 'yan-bindiga ke sace dalibai a makarantun jihar Kaduna ba, abun da ya sa masana harkokin tsaro irin su Dr. Yahuza Ahmed Getso ke ganin akwai barazana a bangaren tsaro.

Idan dai hukumomi su ka tabbatar da cewa adadin daliban da aka sace sun kai 200 kamar yadda al’ummar yankin ke cewa, to daliban za su zama mafi yawa da kuma kankantar shekaru da aka taba sacewa a jihar Kaduna, abun da ke kara saka fargaba a zukatan dalibai da iyaye akan makomar makarantun jihar dake yankunan karkara.

Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara:

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Da Ake Zaton Sun Kai 200 A Jihar Kaduna.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG