Gwamnatin jihar Kaduna dai ta yi Allah-wadai da harin sannan ta ba da umarnin kai agaji yayin da sarakunan yankin ke cewa bayan asarar rayuka, an yi asarar kayan abinci da sutura da gidajen da 'yan bindigan su ka kona.
Tun farko dai da sanyin safiyar ranar Lahadi ne dai 'yan bindiga su ka afkawa garin Gindin Dutse Makyali da ke gundumar Kufanan a Karamar Hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna, inda su ka kashe mutane 12 sannan su ka kona gidaje 17 da su ka hada da rumbunan abinci.
Sai dai sarkin yankin, wato Agwam Kufana, Cif Titus Dauda, ya ce 'yan bindigan ba su sami damar satar mutane ba sakamakon zuwan sojoji.
Kafin wannan hari dai 'yan bindigan sun kai wasu hare-haren a yankunan kananan hukumomin Igabi da Kaura, kuma mukaddashin kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya zagaya yankunan kuma ya ce gwamnati na daukar wasu matakai.
Sace mutane don karbar kudin fansa dai shine sanannen aikin 'yan bindigan daji, kuma ganin a wannan karon an kone mutane da dukiya ya sa masani kan harkokin tsaro Manjo Yahaya Shinko mai-ritaya, bayyana cewa 'yan bindigan na da wata manufa.
A cewar Manjo Shinko harin ya yi kama da na ramuwar gayya ko kuma tsokana.
A baya dai an dan sami saukin hare-haren 'yan bindiga a wasu sassan jahar Kaduna, sai dai dawowar hare-haren jifa-jifa ya sa wasu tunanin cewa aikin 'yan-sa-kai da askarawan da makwabtan jihar Kaduna su ka kirkiro ne ke neman maida hannun agogo baya a jihar Kaduna.
Saurari rahotan Isah Lawal Ikara:
Dandalin Mu Tattauna