Gwamnatin tarayya dai ta fara daukar matakan daidaita hauhawar farashi da tsadar rayuwa amma manyan wasu malaman Addinin musulunci sun ce hanyar da aka fara bi ba za ta bulle ba.
Ko bayan zanga-zangar daidaikun mutane kan tsadar rayuwa dai, ita ma kungiyar Kwadago a Najeriya ta ce za ta yi zanga-zanga a kungiyance saboda halin kuncin da ta ce ma'aikata na ciki.
Ganin yadda aka fara zanga-zangar a wasu jahoshin Najeriya dai ya sa wasu sun fara fargabar juyin-juya hali saboda tsadar rayuwa amma babban malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheik Ahmed Mahmud Gumi ya ce da kamar wuya 'yan-Najeriya su iya hada kai don tunkarar gwamnati kan wannan batu.
Shima masani kan tattalin arziki kuma malami a kwalejin kimiyya da fasaha a jahar Kaduna, Dr. Isma'il Mohammed Anchau ya ce kuncin tattalin arziki a Najeriya ya riga ya kai matuka. Inda ya tabbatar da cewa a tarihi na kusa-kusai dai ba a taba karo da irin wannan tsadar rayuwa a Najeriya ba.
Hajiya Rakiya Bala Tudun Nufawa na cikin masu sharshi kan al-amurran yau da kullun kuma ta akwai hanya mai bullewa masamman idan aka inganta tsaro kuma aka kayyade farashin kayan masarufi a Najeriya.
Masana tattalin arziki irin su Dr. Isma'il Mohammed Anchau kuwa na ganin idan ana so Najeriya ta fice da wannan hauhawar farashi da tsadar rayuwa to wajibi sai an dawo da tallafin mai, a samar da tsaro sannan a magance cin hanci da rashawa.
Ya zuwa yanzu dai zanga-zangar da aka fara a wasu jahoshi ta sa wasu gwamnoni da sauran masu mukamai sun fara tallafawa takawa, abun da wasu ke ganin zai iya rage radadin damuwa kafin daukar matakan dindindin.
Dandalin Mu Tattauna