An sun rarrabuwar kawuna a hadakar kungiyoyin makiyaya a jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya,inda a karon farko wasu kungiyoyin makiyaya suka ce sun yafewa gwamnatin jihar tare da bayyana goyon bayansu ga jam’iyar PDP a zabe mai zuwa, yayin da wasu kungiyoyin kuma ke cewa ba zata sabu ba.
Sakamakon yawan karbar na goro da sojoji ke yi a kan hanya, wani sa'in ma kusan dole, wasu matafiya da kuma direbobi sun gudanar da zanga-zangar lumana tare da datse hanyar Mayo-Belwa zuwa Ganye a jahar Adamawa da ke Najeriya.
Shugaba Buhari ya kwatanta kisan marigayi Badeh a matsayin “babban abin alhini,” yana mai mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin.
‘Ya ‘yan kungiyar ta manyan ma’aikatan jami’o’i ta (SSANU), sun gudanar da zanga-zangar lumana domin mika kukansu game da wasu matsaloli dake damunsu.
Damar ganin likita kyauta da aka baiwa marasa lafiya a jahar Taraba ta janyo dinbin jama'a zuwa birnin Jalingo daga sassan daban-dabam, kuma masu lalurori iri-iri da ke fatan matsalarsu za ta zo karshe.
Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa, wadansu maharan Boko Haram sun kai farmaki a yankin Madagali dake daura da dajin Sambisa inda suka yi kone –kone da harbe harbe.
yanzu haka ana ci gaba da cece kuce da kuma maida martani kan karar da hukumar EFCC ta kai wasu manya 'yan siyasa a jahar Taraba saboda badakalar Naira Miliyan 450 da su ka karba a zaben 2015, ciki har da dan takarar gwamanan APC a shekara mai zuwa.
Dubban jama’a sun halarci bikin nadin Wazirin Adamawa Atiku Abubakar, ciki har da tsoffin shugabannin Najeriya da gwamnoni da kuma sarakunan gargajiya
Mutanen yankin Madagali da Michika sun koka akan lalacewar hanyoyi da gadojin da ke yankin nasu, wanda su ka ce ayyukan da gwamnatin tarayya ta bayar su na tafiyar wahainiya, inada su ka ce yau fiye da shekaru biyu kenan ba wani cigaba na a zo a gani.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama a Najeriya na ci gaba da nuna damuwarsu game da zargin da ake yi a kan lalata da 'yan matan da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu da yanzu ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira, ta hanyar yi musu fyade.
Kamar yadda alkaluman hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ke nunawa kawo yanzu yan gudun hijiran kasar Kamaru da tashe-tashen hankula dake da nasaba da batun yan aware, ya tilastawa guduwa suna barin garuruwansu sun kai dubu talatin.
Kamar yadda siyasa ta gada, bayyana sunayen 'yan takara ke da wuya sai aka shiga jayayya kan sunayen a wasu jahohin da su ka hada da Adamawa
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan kungiyar Boko Haram sun yi shigan burtu inda suka so kai farmaki kan wata makaranta dake Kafin Hausa wajen Bakin Dutse dake yankin na Madagali, to sai dai ‘yan Sakai na maharba sun samu nasarar tarwatsa su.
A karon farko gwamnan jihar Taraba Darius Dickson Isiyaku, ya kai ziyara yankin Mambilla, yanki da yayi fama da tashe-tashen hankali a baya.
kamar yadda 'yan siyasa su ka saba yi, a najeriya, 'yan takarar da su ke ganin ba a masu adalci ba, na ta canza sheka daga wannan jam'iyyar zuwa waccan.
Yayin da hukumar zabe a Najeriya, INEC ke rufe karbar sunayen yan takara da jam’iyu suka mika mata, har yanzu da alamun da sauran rina a kaba a jam’iyar APC, inda a jihohin Adamawa da Taraba ake kai ruwa rana game da batun yan takarar gwamna na jam’iyar.
Kamar yadda al'amarin ya ke a wasu jahohin Najeriya, jahohin Adamawa da Taraba na fama da matsalar sace mutane don nemar kudin fansa.
Al'ummar Madagali da Michika dake jihar Adamawa sun sami kansu a cikin wani halin tsala mai wuya bayan komawa garuruwansu daga gudun hijira samakamakon hare haren kungiyar Boko Haram.
Domin Kari