Yanzu haka Jam’iyyar APC reshen jahar Taraba ta ce ta na mamakin yadda wasu ke nacewa lallai ilele sai an gurfanar da dan takarar ta na gwamna a zabe mai zuwa, wato Sani Abubakar Danladi, kan badakalar Naira Miliyan 450, da tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta bayar domin kamfe din zaben shekarar 2015.
A martanin da jam’iyar ta maida na cece-kucen da ke faruwa game da karar da hukumar EFCC ta shigar a babban kotun tarayya na wadanda ake zargin sun karbi wadannan kudade, jam’iyar ta APC ta yi zargin cewa wasu ne ke neman shafa wa dan takararta kashin kaji.
Mai Magana da yawun Jam’iyar APC na Jihar Taraba, Mr. Aron Arthimas, ya ce dan takarar su Sanata Sani Abubakar Danladi bai dauki kudin bisa kansa ba. Wasu sanatoci biyu ne su ka sa hannu su ka karbi kudin a lokacin, sannan a lokacin ya na rikon gwamnan jahar ya kafa kwamiti na mutune takwas, wadanda su ka jagoranci raba kudin zaben.
Wani lauya mai zaman kansa a Jalingo Barr. Idris Abdullah Jalo ya bayyana abunda doka ke cewa, inda yace ba’a fahimci lamarin ba ne, saboda wanda ake tuhuma ba’a bashi takardar tuhuma ko ta gayyata ba domin ya bayyana a gaban kotu, sannan wadanda su ka kawo karar wato hukumar EFCC bata kawo shi ba.
Ga cikakken rahotan daga Ibrahim Abdul-Aziz
Facebook Forum