Wannan ne karon farko tun bayan dambarwar kafa dokar hana kiwo da gwamnatin jihar Taraban ta kaddamar da gwamnan jihar Arc.Darius Dickson Isiyaku ke samun maslaha da hadakar kungiyoyin makiyaya, inda makiyayan suka mika mubaya'arsu ga gwamnatin PDP a jihar.
Mafindi Umaru Danburam dake zama shugaban kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah mai kula da jihohin arewa maso gabas da ya jagoranci kungiyoyin makiyayan zuwa gwamnatin jihar yace su sun yafe duk abubuwa da suka faru a baya.
A bangarensa kuma, gwamnan jihar Taraban Akitet Darius Dickson Isiyaku ya karyata zargin cewa gwamnatinsa na nunawa musu wariya.
Sai dai kuma yayin da wannan ke faruwa wasu kungiyoyin Fulani sun ce bada yawunsu aka je gidan gwamnatin ba, un kuma ce jam'iyar APC zasu bi. Sahabi Mahmud shine shugaban kungiyar miyetti Allah a jihar ya jagoranci wani taron manema labarai inda suka bayyana matsayinsu da cewa su APC zasu yi ba wata jam’iya ba.
Ga rahoton Ibrahmim Abdulaziz a kan wannan batu daga jihar Taraba:
Facebook Forum