‘Yan bindigan Boko Haram sun kashe fari hula wanda kawo yanzu ba a bayyana irin ta'adin da suka yi ba, koda yake dalibai sun samu nasarar sulalewa.
Wani mazaunin yankin yace hare haren sari-ka-noken da ‘yan bindigan suke kaiwa a wasu yankunan Madagali, hakan na hana manoma da dama gudanar da ayyuka a gonakinsu a cikin wannan lokaci.
Da yake tabbatar da wannan sabon harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai a yankin na Madagali, Mr Adamu Kamale dan majalisar wakilai dake wakiltar Madagali da Michika ya bukaci karin jami' an tsaro domin kare rayuka.
Ya zuwa lokacin aiko da wannan rahoto, hukumomin tsaro a jihar Adamawa basu yi karin haske ba game da lamarin, shi ma mai magana da yawun rundunan ‘yan sandan jihar SP Othman Abubakar yace baida cikakken bayani kasancewar ya yi kokarin jin ta bakin jami'in ‘yan Sandan yankin amma hakarsa bata cimma ruwa ba, yayin da a bangaren sojoji kuma suke cewa basa da hurumin magana sai a Abuja.
A baya makarantu da dama ne 'yan Boko Haram suka kaiwa hari a jihohin Arewa maso gabas, lamarin da ya yi mummunar tasiri a kan harkokin ilimin yankuna, baicin hasarar rayuka.
Ga rahoton wakilin mu Ibrahim Abdulaziz:
Facebook Forum