Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Addabi Manoma A Jihar Adamawa


Wani manomi yana hudar gonarsa da motar tarakta a Kaduna Najeriya.
Wani manomi yana hudar gonarsa da motar tarakta a Kaduna Najeriya.

Al'ummar Madagali da Michika dake jihar Adamawa sun sami kansu a cikin wani halin tsala mai wuya bayan komawa garuruwansu daga gudun hijira samakamakon hare haren kungiyar Boko Haram.

Yayinda al’ummomin da suka koma yankunan su da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram arewacin jihar Adamawa ke kokarin kwashe amfanin gonan da suka noma, ‘yan bindiga masu tada kayar bayan sun bullo da wani sabon salo inda suke bin manoma har gonakinsu suna kashewa da kuma satar amfanin gona.

Al’ummomin yankunan da aka kwaton da yanzu haka ke cikin fargaba, a yankin Madagali da Michika, sun ce maharan na Boko Haram suna yin shigar burtu zuwa gonaki suna kwasan amfanin gona, kuma idan yazo da karar kwana ya kai ga kashe manoman.

Da yake tabbatar da wannan hali da ake ciki, Adamu Kamale dan majalisar wakilai dake wakiltar yankin na Madagali da Michika ya bukaci da kai musu dauki.

Hukumomin tsaro dai a jihar na cewa suna nasu kokari, yayinda suka bukaci al’ummar yankin su bada hadin kai ta wajen kai rahoto da wuri.

Yankin na Madagali bashi da nisa ainun da dajin sambisa dake zama tungar mayakan Boko Haram inda sukan fito domin kai harin sari-ka-noke ko kuma gwabzawa da jami’an tsaro.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul’aziz:

Boko Haram na kaiwa manoma hari a gonaki-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG