Ita dai ziyarar jajen da gwamnan jihar Taraban ya kai yankin na Mambilla, na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka shafe watanni goma sha bakwai da tashe-tashen hankulan, batun da wasu ke dangantawa da siyasa.
Ziyarar kwanaki uku da gwamnan ya kai ya gana da sarakuna da iyayen al’umma da ‘yan siyasa da kuma wasu daga cikin mutanen da lamarin ya shafa, ya kuma bukaci al’umomin yankin su hada kai da kuma yafewa juna.
Al’ummomin yankin sun yaba da wannan ziyarar, yayin da wasu ke suka.
To sai dai kuma tuni aka fara maida martani a ciki da wajen jihar. Gambo Dauda na cibiyar kare hakkin bil adama, ta ‘Centre For Human Rights Advocacy’ ya ce, abin mamaki ne duk da abubuwan da suka yi ta faruwa tun rikicin farko na watan Yunin shekarar 2017, har zuwa na watanin Maris da Afrilu da kuma na watan Mayun wannan shekarar, sai yanzu ne gwamnan jihar ke zuwa ziyarar jaje.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum