Cikin matsalolin dake damun ‘yan kungiyar sun hada da batun rashin cika musu alkawari na kudaden alawus-alawus da suke bi na kimanin Naira Biliyan Takwas.
Kwamared Muhammad Haruna Ibrahim, shine shugaban kungiyar reshen jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Modibo Adama dake Yola, ya ce turace ta soma kaisu bango.
Cikin makwannin nan dai jami’o’in gwamnati a Najeriya, sun yi fama da zanga-zangar lumana da kuma yajin aiki, na baya bayan nan shine wanda kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta gudanar lamarin da ya dankwafar da harkar karatu a jami’o’in.
To wai ko akwai wani wa’adi da kungiyar manyan ma’aikatan suka diba na a share musu hawayensu? Kwamared Muhammad Haruna Ibrahim, ya ce idan har ba a dauki wani mataki ba zasu sake zama domin daukar matakin da ya fi wannan tsauri.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum