Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba hukumomin tsaron kasar umurnin su zakulo wadanda suka kashe tsohon babban hafsan tsaron kasar Alex Badeh mai ritaya.
Umurnin ya fito cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina ya fitar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.
Shugaba Buhari a cewar sanarwa, ya kwatanta kisan marigayi Badeh a matsayin “babban abin alhini,” yana mai mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin.
Ya kuma nuna takaicinsa, kan yadda Badeh ya fada tarkon masu kai hare-hare akan manyan hanyoyin kasar, tare da ba hukumomin tsaro umurnin su kara kaimi wajen samar da cikakken tsaron akan hanyoyin Najeriya.
Buhari ya kuma yaba da irin gudunmuwar da marigayin ya bayar a lokacin yana raye, inda ya ce ya kwashe shekaru sama da 30 yana yi wa rundunar sojin kasar hidima.
Sanarwar ta shugaba Buhari, ta fito a daidai lokacin da gwamnati da kuma al’ummar jihar Adamawa, jihar da Baden ya fito, su ma suke alhinin faruwar wannan lamari.
A wata sanarwa da ita ma ta fitar, gwamnatin Adamawa ta kwatanta lamarina a matsayin abin takaici tare da yin kira da a gudanar da cikakken bincike.
Kwamishinan yada labaran jihar, Ahmed Sajoh, ya bayyana irin bakin cikin da suka shiga sanadiyyar wannan rashi.
"Mun yi bakin ciki matuka, (Badeh) mutum ne wanda a ce ya yi aiki a wurin da ya fi ko ina muhimmanci a harkar tsaro, sannan a ce irin hali na rashin tsaro a ce ya same shi, abin akwai matukar tashin hankali." In ji Sajoh a hirar da ya yi da Muryar Amurka ta wayar tarho.
A jiya Talata wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, suka kai harin kwatan-bauna akan marigayi Badeh, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce, Badeh ya rasu sanadiyar raunukan da ya samu daga harbin bindinga a lokacin da yake tafiya a kan hanyar Abuja zuwa Keffi.
Saurari abin da masana harkar tsaro ke cewa kan wannan lamari da kuma abin da 'yan jihar Adamawa ke cewa a rahotannin Hassan Maina Kaina da na Ibrahim Abdulaziz: