Yanzu haka al’ummomin da su ka koma yankunan na su da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram a yankin Madagali da Michika na jahar Adamawa na kokawa game da aikin kwangilar hanyarsu da gwamnatin tarayya ta bayar, yau fiye da shekaru biyu kenanan da ba da aikin amma har yanzu ya na tafiyar hawainiya, inda kamfanin da aka bawa ayyukan bai ci gaba da aikin.
A daidai lokacin da gadar da ta hada wadannan al’ummomi da sauran sassan jihar ta sake rugujewa bayan gyaran wucin gadin da aka yi wa gadar da itatuwa, wanda wannan gadar ita ta hada Borno, Adamawa, Yobe, Kamaru da Chadi.
Dan Majalisar wakilan yankin ya bayyana cewa wannan lamarin ya dame su, amma sun kai kukansu a gaban majalisa game da yanda dan kwangilar ya shafe shekaru biyu bai yi komai ba. Sannan ya ce za su bincika su ga yadda dan kwangilar ya samu aikin. Ita ma gwamnatin jihar Adamawa ta ce za ta cigaba da bibiyar lamarin
Kungiyar Boko Haram ta lalata hanyoyi da gadoji da dama a yankin wanda, wannan lamarin ya jawo tsaiko a harkokin tsaro da sufuri a yankunan da aka kwato.
Ga wakilin mu na Adamawa Ibrahim Abdul'aziz da cikkaken rahoton:
Facebook Forum