Rundunar sojin saman Najeriya na ci gaba da fatattakar ‘yan bindigar jihar Zamfara, ta hanyar wani gagarumin farmaki da suke kai musu mai taken ‘Operation Dirar Mikiya’.
Babban hafsan hafsoshin rundunar sojojin Afirka ta Kudu ya kai ziyarar aiki Najeriya.
Matsalar fashi da makami da satar mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da addabar matafiya a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A wani yunkurin kawo karshen rikici tsakanin makiyaya da manoma da Kuma satar shanu, gwamnatin jihar Osun zata fara amfani da jiragen da basu amfani da matuka wajen tunkarar al'amarin. Jihar Osun na daya daga cikin jihohin da ake yawan samun rikice rikice tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya. al'amarin da yake haddasa hasarar dubban rayuka da asarara miliyoyin dukiya.
Kungiyar Myetti Allah ta Fulani makiyaya a Najeriya ta nesanta kanta da wa’adin da aka ce ta baiwa shugaban majalisar dattawan Najeriya Dr. Abubakar Bukola Saraki na ya yi murabus ko ta tilasta masa yin murabus.
Kawo yanzu hukumar bada agajin gaugawa ta babban birnin tarayya (FEMA) ta ce ta kammala aikin ceto wadanda rushewar wani bene hawa hudu ya rutsa dasu a birnin Abuja.
Asusun horar da ma'aikata na ITF a Najeriya, ya ce yana hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya a fannin horas da matasa sana'o'i a fannonin ayyuka daban-daban.
Hedikwatar rundunar sojojin saman Najeriya ta ce mayakanta dake fafatawa a jihar Zamfara na ci gaba da murkushe ‘yan bindigar dake addabar jihar.
Bayan umarnin da Shugaba Buhari ya bai wa rundunar sojin saman Najeriya na ta kai manyan jirage jihar Zamfara domin dakatar da kashe-kashen da ake yi a jihar.
Yanzu Manjo Janar Abba Dikko shi ne sabon babban kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole da ke jagorantar yaki da Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabas a Najeriya, yayin da Brigediya Janar O A. Abdullahi da Brigediya Janar U.U Bassey za su jagoranci sashe na 2 da na 3 na rundunar.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce sojojinta sun budewa wasu mayakan kungiyar Boko Haram wuta ta sama a jihar Borno.
Babban bankin duniya tare da hadin gwiwar mahukuntan Najeriya sun bullo da wani shirin tallafawa ‘yan gudun hijirar dake Arewa maso Gabashin Najeriya.
A yayin da masu ruwa da tsaki ke korafi kan karancin 'yan sanda a Najeriya, Kwararru na kalubalantar yadda ake amfani da su a cikin kasar.
A Najeriya ana ci gaba da tafka muhawara dangane da canza shugabannin rundunonin tsaro na kasar musamman duba da yadda matsalar tsaron kasar ke Kara daukar wani sabon salo.
Rundunar sojojin Najeriya ta yi ‘karin haske kan abin da ya sa ‘yan kungiyar Boko Haram ke sace fararen hula su yi garkuwa da su.
Wasu ƴan fashi da makami sun kai harin kwanton bauna inda suka bindige wasu jami'an ƴan sanda guda bakwai a daidai lokacin da suke bakin aiki na bincikar motoci akan shataletalen Galadimawa da ke kusa da kan hanyar filin jirgin saman Abuja.
Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta wanke babban Hafsa mai kula da harkokin mulki na hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya Air vice Marshall Alkali Mamu.
Domin Kari