Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja, darakta janar na
hukumar Joseph Ari ya ce akwai guraben aiki da dama a Najeriya
musamman a bangarorin sana"o"in hannu, to amma Najeriyar bata da
kwararrun da zasu cike guraben. Hakan ya sa asusun na ITF ya shiga wani hadin gwiwa da majalisar dinkin duniya don tabbatar da an horas da isassun matasan da zasu cike wadannan gurabe da ake dasu a kasar.
Joseph Ari yace tuni asusun itf baya ga dubban dubatan matasan da tuni suka horas yanzu haka an tsara sake horas da Karin wasu dubu goma sha uku, kana ya nemi suma gwamnatocin jihohi da su dau nauyin horas da Karin matasan don samar da ayyukan yi.
Darakta janar na ITF din yace ta hanyar sana"o"in hannu ne kadai za a
tabbatar an samar da isassun aikin yi ga matasan Najeriya, domin a
cewar sa gwamnati ita kadai ba zata iya samar da aiki ga kowa da kowa
ba. Daga nan ya nuna rashin jin dadi ganin yadda yan kasashen waje ke
mamaye wuraren aikin da ya kamata ace yan Najeriya ne ke yinsu.
Yayin da yake tsokaci dangane da yadda wasu ke ganin hukumarsa na aiki
iri guda da na hukumar samar da aikinyi ta kasa wato NDE da sauran
hukumomi makamantansu, Sir Joseph Ari yace zai kyautu
azo a zauna a dandale don tantance irin ayyukan da kowacce hukuma
zatafi mayar da hankali akai.
Asusun Horar Da Ma'aikata Na ITF Ya Hada Gwiwa Da Majalisar Dinkin Duniya
Asusun horar da ma'aikata na ITF a Najeriya, ya ce yana hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya a fannin horas da matasa sana'o'i a fannonin ayyuka daban-daban.
WASHINGTON DC —
Facebook Forum