Wani sabon salo da masu satar mutane na kan hanyar Abuja zuwa Kaduna suka dauka, shi ne budewa motoci wuta kafin su tsayar da su.
A ranar Asabar din da ta gabata sai da wasu matafiya suka yi kicibis da masu satar mutanen, da yake zantawa da Muryar Amurka, Abubakar Barau, da yake daya daga cikin mutanen da suka hadu da ‘yan bindigar, ya ce Allah ne kawai ya tsarar da su, domin kuwa yayin da suka isa wajen da ‘yan bindigar suke sun bude musu wuta, wanda ganin hakan barazana ne ga rayuwarsu ya sa ya nufi kan daya daga cikinsu, shi kuma ya kaucewa hanya.
Sai dai kuma bayan da su Abubukar suka tsallake rijiya da baya, sun tarar da ‘yan sanda a Katari, suka kuma bayar da rahotan abin da ya faru da su. Amma sai ‘yan sandan suka shaida musu cewa basu da kayan aikin da zasu iya fuskantar ‘yan bindigar, da suka hada da harsashi da mai a mota da dai sauransu.
Muryar Amurka ta yi kokarin tunbutar jami’an ‘yan sanda, amma ba a samu nasara ba.
Masana tsaro irin su Kwamanda Musa Isa Salmanu mai ritaya, na ganin hanyar kawai da za a iya tunkarar wannnan matsalar itace ta hanyar hada karfi da karfe tsakanin mahukunta da Jami’an tsaro da kuma mutanen gari.
Ganin cewa mutanen dake aikata irin wannan ta’asa mutane ne da aka sani, kuma yana da matukar muhimmanci da zarar an baiwa jami’an tsaro irin wannan bayanai su rika bin diddigin lamarin.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum