Tsohon ministan 'yan sandan Najeriya a lokacin Shugaba Jonathan, Alhaji Adamu Maina Waziri ya bayyana cewa a lokacin da ya kama aiki a 2010, an shaida masa adadin jami'an 'yan sanda ya kai dubu dari uku da saba'in da bakwai, amma kafin ya bar aiki, kididdigarsa ta nuna masa tsakanin dubu dari uku zuwa dubu dari uku da talatin.A lokacin yawan jama'ar kasar ya kasance kusan miliyan 160.
"Babu yadda za a yi a ce mutum dubu dari uku in ma da saba'in da bakwai din ne sun bada tsaro ga al'umma miliyan 160, " inji Waziri.
Ya ci gaba da bada misali da kasar Masar, " Tana da mutane miliyan 80 amma wadanda ke aikin 'yan sanda mutum ne miliyan 4. Amma hakan bai hana aikin ta'addanci a kasar ba. Saboda haka 'yan sandan Najeriya sun yi kadan."
A kuma irin wannan karanci ne, masu sharhi irinsu Shu'aibu Mungadi ke kalubalantar yadda shugaban 'yan sandan ke tsara salon tsaron a halin yanzu.
A cewarsa, " ba aikin hankali ba ne kuma ba nuna tausayi ba ne a ce ranar da aka yi kisan kiyashi ga al'ummar Sokoto, ban ji labarin an kara 'yan sanda ko da guda uku ba a jihar Sokoto amma an dauki 'yan sanda dubu talatin an kai jihar Ekiti domin zabe."
" Wannan ya nuna rashin imani da tausayi da kuma rashin kiyaye dokokin aikin 'yan sanda." inji Mungadi.
Shi ko kakakin sufeto janar na Najeriya, Bala Ibrahim cewa yayi jama'a basu fahimci yadda harkar tsaro take ba.
"Watakila kuma an jahilci yadda aikin zabe yake. Idan ka duba wannan zabe da akayi, aka kai 'yan sanda dubu talatin, a zabe na baya na 2014, an kai 'yan sanda dubu 75 ne, wanda sun ninka wannan adadi sau sama da biyu. Amma harkar zabe ta banbanta da harkar tsaro ta yaki da ta'addanci da sauransu," inji shi.
To wane mataki shi sufeto janar ke dauka a Zamfara, Birnin Gwari da sauransu?
"A Zamfara an tura jami'an tsaro sama da dubu 6, Birnin Gwari an tura kusan dubu 7," inji Bala Ibrahim.
Facebook Forum