Gwamnatin jihar Osun yanzu haka ta bullo da shirin yin amfani da fasahar zamani inda za a fara aiki da jirage marasa matuka, don gano duk inda masu satar shanu suke. Haka Kuma za a samar da layukan waya da za a rika bugawa kyauta don sanar da hukuma yayin da shanu ke barna a gonaki tare da daukar mataki a hukumance.
Wani masanin tsaro Mallam Kabiru Adamu, ya ce wannan mataki ne mai kyau, amma matsalar ita ce, yadda za ayi amfani da bayanan wannan jirge, kasancewar jihar bata da jami'an tsaro na kanta, ya ce muddin ana son samun nasara to akwai bukatar fadakarwa da kuma wayar da kan dukan bangarorin biyu tun da don su ake yi ta yadda zasu bada hadin kai.
A nasu bangaren kungiyoyin makiyaya da manoma, na maraba lale da wannan mataki wanda suka ce zai taimaka masu. Hounarable Khalil Mohammed Bello, shugaban kungiyar makiyaya ta Kullen Allah' na kasa,
ya ce, lalle wannan shiri zai taimaka kwarai, kana ya nemi gwamnatoci a
dukkan matakai da suyi koyi da gwamnatin jihar Osun na daukar irin
wannan mataki.
Shima Mallam Musa Labaran Wamba na kungiyar manoma ta Najeriya ya ce tabbas wannan tsari na gwamnatin jihar Osun abin a yaba ne, saboda wannan mataki na iya kawo zaman lafiya.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum