Rahoton wata cibiyar bincike dake nan birnin Washington DC, da ake kira Brookings Institute, ya nuna cewa kasar Syria itace kan gaba inda mutum dubu 260 suka rasa rayukansu sakamakon tarzoma. Sannan kuma sai Afghanistan da Iraqi da Najeriya da kuma Yamal.
Shugaban cibiyar bunkasa dimokaradiyya da ci gaba a Najeriya, Dakta Shettima, ya ce rahotan ko kadan bai bashi mamaki ba, ganin irin ta’addancin da kungiyar Boko Haram ta yi a kasar, haka kuma an zargi sojojin kasar da laifin kashe mutane.
Shima a nashi tsokacin, wani masanin tsaro, Kwamanda Musa Isah Salmanu, na cewa wannan rahota zai iya zama gaskiya idan aka dubi irin yadda aka yi ta kashe al’umma.
Sai dai kuma kwararru irinsu mallam Muhammad Ibrahim Damaturu, na tababar sakamakon wannan bincike na cibiyar Brookings, wanda ke cewa abin ya bashi mamaki domin irin yake-yaken da ke faruwa a kasasehen larabawa ba za a iya kwatanta shi da abin da ya faru a Najeriya ba.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum