Tun farko dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya baiwa rundunar sojin saman kasar umarnin daukar manyan jiragen yaki zuwa jihar Zamfara domin kawo karshen kashe-kashen da ya ta’azzara a jihar.
Mallam Ibrahim Janyau, dake zama shugaban wata kungiyar samar da zaman lafiya a Zamfara, ya nuna gamsuwarsu da aikin da sojojin saman kasar ke yi a yankunansu. Ya kuma bayar da missali da garin Munaka dake gundunar Mada, inda wani jirgin yaki yayi shawagi a yankin, inda hakan yasa ‘yan bindigar suka gudu cikin karkara.
Sai dai kuma yayin da sojojin ke ci gaba da murkushe ‘yan bindigar, ana ci gaba da samun kwarar ‘yan gudun hijira zuwa Katsina mai makwabtaka da jihar ta Zamfara.
Majiyoyi daban-daban sun tabbatarwa da Muryar Amurka cewa gwamnatin Katsina na taimakawa ‘yan gudun hijirar, kamar yadda shima gwamnnan Katsina Aminu Bello Masari, ya tabbatarwa da wakilin Muryar Amurka.
Gwamna Masari, ya tabbatar da cewa da kansa ya ziyarci wajen da ‘yan gudun hijirar suke, domin gano hanyar da zasu ‘kara taimakawa ‘yan gudun hijirar.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum