Duba da yadda tarzomar kungiyar Boko Haram ta daidaita shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya, bankin duniya zai kashe dalar Amurka Miliyan 75 don gudanar da aikin farfado da yankin.
Cikin wannan makon ne aka gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki don bitar yadda shirin ke kankama, da kuma tabbatar da ganin samarwa ‘yan gudun hijirar ababen more rayuwa.
Wannan shiri dai ya mayar da hankali ne domin ganin an samar da rayuwa ga mutanen da aka raba da muhallansu, ta hanyar sake gina gidaje da samar da asibitoci da kuma makarantu.
Babban manajan shirin a jihar Borno, Alhaji Usman Ciroma, ya tabbatar da cewa hakiki suna amfana da wannan shiri, inda yanzu haka a jihar Borno wasu kananan hukumomi da aka fara ayyukan suka fara cin moriyarshi.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum