kakakin gwamnatin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango, ya ce, shugaba Jospeh Kabila, na da niyyar ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar tare da shirin mika mulki bayan an kammala zabe
Manyan ‘yan jam’iyar Democrat a kwamitin Majalisar dokokin Amurka da ke kula da fannin tattara bayanan sirri, sun zargi mambobin kwamitin ‘yan Republican da sauya wasu bayanai da ke cikin wasu takardun da ke dauke da matsayar da aka cimma, kafin su aika Fadar White House ta shugaban Amurka.
Tashin hankalin da Sudan ta Kudu ta jima tana fama da shi ya janyo mata matsalar karancin kudaden tafiyar da al’amurra inda har ma’aikatan ofisoshin jakadancin kasar a kasashe da dama suka jima babu albashi.
Rundunar sojin Amurka da ke yankin Afirka ta AFRICOM, ta ce tana sane da hotunan da aka dora a shafin Twitter kuma tana yin dubi kansu domin ta tantance gaskiyar lamarin na cewa ko akwai wani faifan bidiyo mai alaka da sojojinta da aka kashe a Nijar.
Shugaban Amurka Donald Trump yace a shirye yake ya amsa duk wata tambayar da za’ayi mishi a binciklen da babban Lauya na musamman Robert Muller ke gudanarwa akan zargin da ake na shisshigin Rasha a zaben Amurka na shekarar 2016.
Shugaban Kasashen duniya sun hallara a birnin Davos da ke kasar Switzerland domin halartar taron tattalin arzikin na duniya.
Kungiyar kare hakin bil’adama ta Human Rights Watch ta fitar da rahoton ta na shekarar 2018, inda ta yi kira ga shuwagabani su yaki yan siyasa masu rayin kama karya dake rabewa da guzuma domin su harbi karsana.
Shugaban Zimbabwe Emerson Mnangagwa ya ce za’a gudanar da zabe a kasar nan da watani 4 zuwa 5, zabe na farko tun baya da aka hambarar da dadadden shugaban kasar Robert Mugabe.
Ma’aikatar harkokin wajen Syria ta fada a yau Alhamis cewa kasancewar sojojin Amurka a Syria tamkar tsokanar fada da kuma keta diyaucin kasar ne
Hukumomi a Jihar California dake yammacin Amurka sun ce sun kama wani mutum da matarsa sakamakon samun su da lafin daure 'ya'yansu 13 a matsayin fursnunoni a muhalli mai tsananin kazanta.
Amurka da Canada suna daukar dawaniyar wani taro yau Talata a birnin Vancouver wanda zai maida hankali kan matsawa Koriya ta Arewa lambar ta yi watsi da shirye shiryen ta na Nukiliya.
Yau Talata, Jami’ai da ‘yan sanda a Nigeria suka kiyasta cewa mutane 80 aka kashe tun 31 ga watan Disemba izuwa yau, sakamakon tashe tashen hankula tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gayawa manyan yan majalisar dokoki a yau Talata cewar zai amince da duk wata doka da majalisa ta yarda da ita na kare dubban yara bakin haure
An harbe wani sanannen dan siyasar Serbiya a Kosovo, Oliver Ivanovic har lahira yau Talata a wajen offishin jami'iyyarsa dake garin Mitrovica a arewacin kasar.
Ministar harkokin waje ta kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini tace yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran kan shirin Nukiliyar kasar tana aiki.
Harin kunar bakin wake a wani sansanin soja dake kudancin Afghanistan yau Laraba, ya kashe akalla sojoji biyu tare da raunata wasu su 15
Wannan musanya ita ce ta farko cikin watanni, kuma ta kunshi musanyar fursunoni kusan 400 a tsakanin sassan guda biyu
Ministocin harkokin wajen Amurka da Rasha sun bayyana cewa ba su yarda a ce Koriya ta Arewa ta mallaki makamin nukiliya ba, kuma sun amine da su cig aba da aiki tare domin neman hanyar dakatar da shirin nukiliyar kasar.
A yayin da ake dab da shiga sabuwar shekarar 2018, 'yan Najeriya sun zura ido suna tsumayin abin da gwamnati zata tanadar musu domin samun saukin rayuwa.
Mutum hudu ne aka tabbatar an kashe a wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai garin Kamale da ke yankin Michika, daya daga cikin kananan hukumomin da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram a arewacin jihar Adamawa.
Domin Kari