Manyan ‘yan jam’iyar Democrat a kwamitin Majalisar dokokin Amurka da ke kula da fannin tattara bayanan sirri, sun zargi mambobin kwamitin ‘yan Republican da sauya wasu bayanai da ke cikin wasu takardun da ke dauke da matsayar da aka cimma, kafin su aika Fadar White House ta shugaban Amurka.
‘Yan Democrat sun ce kamata ya yi, su aika da takardun da aka gabatar aka kuma amince da su a gaban majalisar, wadanda aka kada kuri’a akansu.
An yi zargin cewa takardun wadanda Fadar ta White House za ta iya fitar da su a yau Alhamis a baina jama’a, suna dauke da bayanan ma’aikatar shari’ar kasar, wadanda suka bayyana son kai da aka nunawa shugaba Trump.
Dan majalisar wakilai, Adam Schiff ne ya bayyana a wata wasika da ya aike wa shugaban kwamitin Devin Nunes a jiya Laraba cewa, ‘yan Democrat sun gano cewa an sauya bayanan da ke cikin takardun, lamarin da ya kwatanta a matsayin “mai ta da hankali.”
Sai dai wani mai magana da yawun Nunes din ya fitar da wata sanarwa da ke nuna cewa, an “dan yi sauyi” a kwapin da aka aika wa Fadar White ta Shugaban Amurka.
Sanarwar ta kara da cewa, ‘yan Democrat din suna so ne su kau da hankalin jama’a daga kan batun cin zarafin da ke cikin takardun.
Facebook Forum