Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Manyan Kasahen Duniya Akan Shirin Nukiliyar Iran Na Aiki


Rouhani da Fedrica Mogerini a Iran
Rouhani da Fedrica Mogerini a Iran

Ministar harkokin waje ta kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini tace yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran kan shirin Nukiliyar kasar tana aiki.

Ministar harkokin waje ta kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini tace yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran kan shirin Nukiliyar kasar tana aiki, tace duk da cewa akwai damuwa kan cewa Iran tana kera makamai masu Linzami da wasu take-taken ta a gabas ta tsakiya,wadannan batutuwa ne da za’a iya tunkarar su daban daga yarjejeniyar.

Ta yi magana ne bayan taron da ministocin harkokin wajen Britaniya, a Faransa, da Jamus, da Iran suka yi a Brussels, danagne da yarjejeniyar ta 2015, wacce ta takaita shirin Nukiliyar Farisar, saboda fargabar tana kokarin kera makaman Nukiliya, aka saka mata ta wajen janye takunkumin karya tattalin arziki da aka kakaba mata.

Iran ta dage cewa shirin Nukiliyarta na farin kaya ne. Ministan harkokin wajen kasar Javad Zarif, bai fito gaban ‘yan jarida da sauran takwarorinsa ba, amma jiya Laraba ya bayyana goyon bayansa ga yarjejeniyar, yayinda kuma ya zargi a Amurka da aiwatar munanan manufofi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG