Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbe Wani Sanannen Dan Siyasar Serbiyawa A Kosovo, Oliver Ivanovic


An harbe wani sanannen dan siyasar Serbiya a Kosovo, Oliver Ivanovic har lahira yau Talata a wajen offishin jami'iyyarsa dake garin Mitrovica a arewacin kasar.

An harbe wani sanannen dan siyasar kabilar Serbiyawa na Kosovo, Oliver Ivanovic har lahira yau Talata a wajen offishin jam'iyyarsa dake garin Mitrovica a arewacin kasar, wanda ya janyo zaman dar dar a yankin har ya sa aka dakatar da tattaunawar sulhu tsakanin Kosovo da Serbia a ranar da ya kamata a ci gaba da tattaunawar.

‘Yan sanda sun ce wasu 'yan bindiga daga cikin mota ne suka harbi Ivanovic, mai shekara 64 da haihuwa, a lokacin da ya isso shelkwatar jam'iyyar. Sun bayyana cewa sun gano wata mota da ta kone da suke tunanin motar da aka yi amfani da ita wajen gudanar da harin ce.

Lamarin ya auku a ranar da aka shirya komawa ga yin shawarwarin sulhu tsakanin Serbia da Kosovo a Brussels domin dawo da kwanciyar hankali. Bayan harin, Serbia ta janye daga zaman sulhun.

Jami’ar dake lura da manufofin kasashen waje ta Kungiyar Tarayyar Turai, Federica Mogherini, ta la’anci kisar ta wayar tarho a lokacin da take Magana da Shugaban kasar Serbia Aleksandar Vucic da shugaban kasar Kosovo Hashim Thaci, inda ta ce tana fatar hukumomi za su nemo wadanda suka kai harin kuma za’a hukunta su.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG