Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Sun Koka Da Halin Talauci Na Rayuwa


Mutane A Kasuwa
Mutane A Kasuwa

A yayin da ake dab da shiga sabuwar shekarar 2018, 'yan Najeriya sun zura ido suna tsumayin abin da gwamnati zata tanadar musu domin samun saukin rayuwa.

'Yan Najeriya sun ce kokarin yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Najeriya ke ta yi, ya sa mutane cikin Ukuba da talauci.

Kawo yanzu gwamnati ta ce ta kwato milliyoyin daloli da billiyoyin naira tare da kadarori daga hannun tsoffin jami'an gwmanati da ke fuskantar shari'a. Sai dai kuma a yayin da gwamnati ke yakar cin hanci da rashawa hakan ya haifar da ukuba ga al'umma.

Matakan da babban bankin Najeriya ta dauka akan kudin Naira ya yi tsanani hakan ya sa mutane su ka koka da tsadar rayuwa da talauci. Amma wasu na ganin cewa idan aka yi hakuri za 'a wuce gangin da aka tsinci kai a ciki.

Wasu da dama sun yi kira ga gwamnati da taimaka wajen samarda sassauchin abubuwan more rayuwa.

Ga Babangida Jibrin da cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG