Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya isa birnin Davos da ke Switzerland domin halartar taron tattalin arzikin na duniya.
Trump zai kasance shugaban Amurka na farko da ya halarci taron sanda yake kan mulki bayan ahugaba Bill Clinton da ya je a 2000.
Manazarta sun ce wakilai da yawa sun daura damarar jan daga akan sabanin ra’ayoyinsu kan yadda kowannensu ke kallon halin da tattalin arzikin duniya yake ciki.
Ana sa ran cewa Shugaba Trump zai yi kokarin tallata akidarsa ta maida Amurka ta farko, wanda ya sa Amurka ta saka haraji kan kayayyakin da ake shiga da su cikinta.
Sannan Amurka za ta nemi ta sauya tsarin cinikayyarta da sauran kasashen duniya.
Amma sauran manyan kasashen duniya kamar na nahiyar Turai da China da Japan, na kira da a sake sabon tsari na sassauta matakan kasuwanci tsakanin kasashe.
Facebook Forum