A halin da ake ciki kuma Shugaban Amurka Donald Trump yace a shirye yake ya amsa duk wata tambayar da za ayi mishi a binciklen da babban Lauya na musamman Robert Muller ke gudanarwa akan zargin da ake na shisshigin Rasha a zaben Amurka na shekarar 2016.
A watanin baya da suka wuce, Trump yace zai amince dari bisa dari su gana da masu binciken Mueller amman daga baya kuma ya dawo yana tambaya dalilin da yasa ake son a zauna a tattauna dashi tunda babu wata muna muna.
Mueller yana son ya tattauna da shugaba Trump ne akan korar da yayi wa tsohon shugaban hukumar binciken sirri ta FBI James Comey da kuma tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro Michael Flynn.
Mueller dai yana bincike ne akan ko Trump yayi abinda ya sabawa doka a lokacin da Comey yace a farkon shekarar 2017 inda aka ce Trump yace mishi ya ajiye binciken da yake akan dangantakar da Flynn yake da ita da jakadan Rasha a birnin Washington.
Alakar da ake zaton ta kullu ne makonni kadan kafin Shugaba Trump ya fara mulki a shekarar data gabata, sannan bayan watanni, ya kori Comey wanda a lokacin shine shugaban binciken da akeyi kan zargin da ake yi wa Rasha.
Facebook Forum