Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Sojoji Biyu Tare Da Raunata Wasu 15 A Afghanistan


Harin kunar bakin wake a wani sansanin soja dake kudancin Afghanistan yau Laraba, ya kashe akalla sojoji biyu tare da raunata wasu su 15

Wani harin kunar bakin wake a wani sansanin soja dake kudancin Afghanistan yau Laraba, ya kashe akalla sojoji biyu tare da raunata wasu su 15.

Harin ya faru ne a Lashkargah, babban birnin lardin Helmand dake fama da rigingimu kusan kullum, kuma aka auna wani gungun sojojin Afghanistan ne wadanda ke shirin barin sansanin don kai farmaki akan ‘yan Taliban a wata gunduma dake kusa.

Wani mai magana da yawun gwamnatin lardin, Omar Zwak ya fadawa muryar Amurka cewa wasu ‘yan kunar bakin wake biyu sun shiga wata mota da aka dankarawa nakiyoyi amma jami’an tsaro suka dakatarda su kafin su shiga sansanin soja, abinda ya sa suka tada ababen fashewar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG