Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana kasar Uganda a matsayin wacce ta rabu da cutar Ebola, kwanaki 42 tun bayan samun mutum na karshe da ya kamu da cutar.
Tun bayan komawar Najeriya kan tsarin mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999 har ya zuwa yanzu, muhimmin abin da ya fi daukar hankanli shi ne rashin samun wakilcin mata a harkokin siyasa, duk da cewa bincike ya bayyana mafi yawan masu kada kuri’u a ranar zabe mata ne da matasa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin gwamnatin sa na karshe, yayinda ake ci gaba da fama da kalubalen tsadar rayuwa a kasar ta Afirka ta Yamma mai arzikin man fetir kuma mafi yawan bakar fata a duniya ba.
Mutanen da ambaliyar ruwa ta lalata musu gonaki da gidaje a jihar Kano da ke Najeriya na ci gaba da korafi kan yadda hukumomin jihar da-ma na tarayya suka yi watsi da makomar su.
Kwamitin Kula da Harkokin Makamashi a Majalisar Wakilan Najeriya ya yi taron sauraren ba'asin jama'a kan yunkurin gyara dokar samar da wutar lantarki ta shekara 2005, don samar da tsarin doka da daidaita aiwatar da ayyukan samar da wutar lantarki.
‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’yoyi mabanbanta kan goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya sanar.
Wannan dai shi ne karon farko cikin shakaru 100 da wanda ake ganin zai zama kakakin majalisar wakilai ya gaza lashe zaben kujerar a zagayen farko.
Ana dada samun karin bayani kan musabbabin rasuwar shahararren dan wasan kwallon kafan nan na kasar Brazil, Pele
Kamfanin Twitter ya dakatar da hada dandalin da manyan shafuka irinsu Facebook da Instagram, da abokan hamayyarsa Mastodan, Tribel, Nostr, Post, da Truth Social na tsohon shugaban kasa Donald Trump.
Amurka na shirin bai wa kasashen Afirka dala biliyan $55B nan da shekaru uku masu zuwa, kamar yadda jami’an Fadar White House suka bayyana.
Gobe Talata ake shirin fara babban taron manyan ‘yan kasuwa da shugabannin kasashen Afirka 49, da kuma kusoshin gwamantin Amurka, ciki har da Shugaba Joe Biden wanda shi zai jagoranci bukin buden taron.
Kylian Mbappe za su sake haduwa da babban abokinsa Achraf Hakimi a gasar cin kofin duniya.
Morocco ta kafa tarihi na zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya, bayan da ta ci Portugal 1-0 a wasan Quarterfinals.
An kammala taron bita da kara wa juna sani na yini uku a Kano ga kwamandoji da sauran manyan Jami’an hukumomin Hisbah na jihohi 6 a arewa maso yammacin Najeriya.
Domin Kari