Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Joe Biden ke karbar bakuncin taron yini biyu da shugabannin Afirka.
Alkawarin tallafin na shekaru uku na Amurka ya kunshi dala biliyan $20B don shirye-shiryen kiwon lafiya.
Da yake jawabi ga shugabannin Afirka jiya Laraba a taron kasuwanci, Shugaba Joe Biden ya ce Amurka na kan gaba ga makomar Afirka nan gaba, kuma ya sanar da sabbin damarmakin kasuwanci da alkawuran samar da ababen more rayuwa, da suka hada da samar da makamashi mai tsafta da tattalin arzikin zamani.
Biden ya ce “Habaka ababen more rayuwa na Afirka yana da muhimmanci ga burinmu na gina ingantaccen tattalin arzikin duniya, wanda zai fi dacewa da irin matsalolin da muka gani a cikin ‘yan shekarun da suka gabata.”
Shugaban na Amurka yana fuskantar wasu soke soke na rashin ganawa da shugabannin na Afirka da ya karbi bakunci daya-daya.
Jami’an gwamnati sun ce nan ba da jimawa ba, Biden da mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris da wasu sakatarorin majalisar zartarwa za su kai ziyara Afirka, domin tattaunawa dalla-dalla.