Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Majalisar Wakilan Amurka Ta Gaza Zaben Shugaban Ta


Dan Majalisar Wakilai Kevin McCarthy
Dan Majalisar Wakilai Kevin McCarthy

Wannan dai shi ne karon farko cikin shakaru 100 da wanda ake ganin zai zama kakakin majalisar wakilai ya gaza lashe zaben kujerar a zagayen farko.

Majalisar Wakilan Amurka ta kasa zabar kakakin majalisar na gaba a ranar Talata, yayin da gungun ‘yan majalisar dokokin Amurka masu ra’ayin rikau ke ci gaba da kada kuri’ar kin amincewa da yunkurin dan jam’iyyar Kevin McCarthy na jagorantar zauran majalsiar na 118. Bayan kada kuri’a zagaye na uku, majalisar ta dage zamanta har zuwa ranar Laraba don ci gaba da aiki.

Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 100 da babu wani dan jam’iyyar Republican ko Democrat da ya lashe zaben kakakin majalisar a zagayen farko na zaben zama shugaban majalisar mai wakilai 435.

'Yan Majalisar Dokokin Amurka
'Yan Majalisar Dokokin Amurka

McCarthy ya gaza lashen kujerar kakakin majalisar a zagaye uku da aka kada kuri’a, inda ‘yan Republican 20 suka nuna adawa da shi a zagaye na karshe. Zaben zagaye na hudu yana kan hanya, amma babu tabbas ko masu adawa da McCarthy za su yi watsi da adawar su bashi goyon baya, ko kuma za a samu sabbin ‘yan takara su fito.

‘Yan jam’iyyar Republican za su samu dan karamin rinjaye da wakilai 222 a kan ‘yan Democrat 212 a majalisar, tare da gurbi daya da a halin yanzu, dan majalisar na jihar California na tsawon shekaru 16, McCarthy yake bukatar akalla kuri’u 218 don zama kakakin majalisar. A karkashin wani tanadi na kundin tsarin mulkin Amurka, zai zaman na biyu a jerin masu maye gurbin shgabancin Amurka.

Dan Majalisar Wakilai Jim Jordan Da Sauran 'yan Majalisa a zauran majalisar
Dan Majalisar Wakilai Jim Jordan Da Sauran 'yan Majalisa a zauran majalisar

Amma ‘yan Republican 19, wanda da dama a cikinsu suka bayyana ra’ayin a cikin ‘yan makonin nan cewa, McCarthy ba cikakken dan ra’ayin mazan jiya ba ne da zai jagoranci ‘yan Republican a majalisar, inda suka zabi wasu ‘yan majalisar Republican a zagayen farko na kada kuri’a, cikin har da dan majalisa Andy Biggis na jihar Arizona da Jim Jordan na jihar Ohio, wanda dukkanin su masu adawa ne da shugaba Joe Biden na Democrat.

A zagayen kuri’ar na uku, ‘yan Republican 20 masu adawa sun zabi Jordan, duk da cewa shi kansa ya amince da McCarthy a matsayin zabinsa na jagoran ‘yan Republican masu rinjaye a sabuwa majalisa mai wa’adin shekaru 2.

'Yan Majalisar Dokoki Amurka
'Yan Majalisar Dokoki Amurka

Dan majalisar wakilai na jam’iyar Democrat Hakeem Heffries daga jihar New York, da dukkan ‘yan Democrat suka zabe shi, shi ne ya jagorance su a zaben kakakin majalisar, ko da yake ba shi da damar yin nasara saboda babu wani dan Republican da ke shirin zaben sa.

A zaben baya bayan nan, yan Republican 202 ne suka zabi McCarthy, inda ya gaza samu kuri’a 16 ya cika 218 da yake bukata.

XS
SM
MD
LG