Sai dai wani babban kalubale da ake dangantawa da hakan shi ne rashin nuna goyon baya da mata ke yiwa yan’uwansu mata, yayin neman wani mukami na siyasa a Najeriya.
A halin da ake ciki mata miliyan 6.2 cikin mutum miliyan 12.2 ne suka yi rejistar katin kada kuri’a gabanin zabe a Najeriya da ke tafe, lamarin da ke nufi da cewa, su ke da kusan kashi 50 cikin 100 na kuri’un al'ummar kasar kenan.
Amma duk da wannan tasirin da matan ke da shi a zaben kasar har yanzu da sauran aiki a gaba wajen samun manyan mukaman siyasa don wakilcin al’umma.
Batun da ‘yar takarar gwamnan a jihar Jigawa karkashin jam’iyyar Action Alliance, Hajiya Binta Umar, ta ce a halin da ake ciki mata sun fahimci cewar su ake cuta kuma su ake bari a baya don haka dole ne su tashi daga barcin da suke yi.
Wani dan siyasa a Najeriya, Hon. Saidu Gombe, ya ce mafi yawa matsalolin mata idan mace ta fito ba su cika mara mata baya, a maimakon haka sai su rika mata kiyayya na kin su zabe ta. Ya ce da mata za su hade su zabi jinsun su mata da an samu wakilcin mata da yawa.
Sai dai a cewar, Mrs Dorathy Akin Ova, wacce ita ma ta fito neman kujerar shugabancin kasar na shekarar 2023 hakan bai sanyayawa mata gwiwa ba duk da itama bata kai labari ba a zaben fidda gwani na jam’iyyar SDP da ta fito, ta ce wannan karon za’a ga banbanci.
Itama Hajiya Khadija Iya Abdullahi daya daga cikin matan da ke neman kujerar gwamna a jihohi 17 da ke fadin Najeriya daga jihar Neja ta bayyana cewa babu gudu ba ja da baya duk da kalubale da mata ke fuskanta a siyasar Najeriya.
Idan za’a iya tunawa a shekarar 2007 ne, Mrs Serah Jibril, karkashin jam’iyya PDP ta fito amma bata kai labari ba kasancewa ita kadai ta zabi kanta a lokacin zaben fidda gwani duk da cewa akwai mata da dama cikin wakilai jam’iyyarta.
Tuni dai Hukumar zabe ta INEC ta jaddada kudirinta na wayar da kan mata kan lamuran da ya shafi zabe, kamar yadda babban jami’a a sashen yada labarai ta hukumar Zainab Aminu Abubakar ta bayyana.
Gabanin babban zaben kasar da ke tafe, mata 381 ne kacal cikin yan’takara dubu 4,259 ke neman kujerar shugabancin kasar da na majalisar dokokin, lamarin da ke nuni da cewa, akwai sauran gibi sosai wajen wakilcin mata a mukaman siyasar Najeriya
Saurari cikakken rahotonShamsiyya Hamza Ibrahim: