WASHINGTON D.C. —
Shirin noma tushen arziki na wannan makon, zai kawo muku bita kashi na biyu, a cikin jerin shirye shiryen da muka gabatar muku a wannan shekarar da muke ban kwana da ita. Shirin ya duba farashin kayayyakin abinci a Najeriya da Jamhuriyar Nijar, bayan fara azumin watan ramadan.