Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Sa Hannu A Kasafin Kudi Na Karshe


Shugaban Najeriya yayin da yake sanya hannu kan kasafin kudin 2023 (Facebook/Bashir Ahmad)
Shugaban Najeriya yayin da yake sanya hannu kan kasafin kudin 2023 (Facebook/Bashir Ahmad)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin gwamnatin sa na karshe, yayinda ake ci gaba da fama da kalubalen tsadar rayuwa a kasar ta Afirka ta Yamma mai arzikin man fetir kuma mafi yawan bakar fata a duniya ba.

Najeriya na daya daga cikin kasashen duniya da ke da albarkatun kasa da ma’adinai harma da kasar noma, amma ‘yan kasar na fama da talauci da kuma tsadar rayuwa.

Tsadar kayan masarufi na ci gaba da zama abin damuwa yadda hatta mai matsakaicin samun kudin shiga a kasar bashi da halin iya cin abinci sau uku a rana.

KEBBI: Shinkafa da sarafata
KEBBI: Shinkafa da sarafata

Duk da cewa gwamnatin Najeriyar ta fitar da wasu tsare-tsare na tallafawa manoma don bunkasa harkar noma, daya hada da rufe iyakokin kasar don habaka noman shinkafa, kasancewar ta daya daga cikin kayan abinci da ‘yan kasar suka fi amfani da ita.

Sai dai kuma kwalliya bata biya kudin sabulu ba don shinkafar tayi tsadar da take kokarin gagarar al’ummar kasar da dama.

Wasu 'yan Najeriya sun ce wannan tsadar kayan masarufin ta sa 'yan Najeriya cikin matsannacin hali ba ma’aikata kadai wadanda albashin na su bai takara kara ya karya ba, har da 'yan kasuwa tun da sai anyi musu cinikin hajarsu sannan su samu abun kai wa iyalan su.

KEBBI: Shinkafa da sarafata
KEBBI: Shinkafa da sarafata

A hirar shi da Muryar Amurka, masanin tattalin arziki a Abuja, Yusha’u Aliyu, ya ce abubuwa da dama ne su ka haifar da tsadar kaya musamman shinkafa. Daga cikin su akwai iftila’in ambaliyar ruwa, da yadda kamfanonin suke tura wakilansu wurare da dama suna sayen shinkafar, da kuma wasu mutane da dama da suka mayar da shinkafar abincin da ake ci safe da rana, shi yasa wannan ya haifar da bukatunta da yawa.

A na sa bangaren, mai sharhi kan lamuran yau da kullum kwamred Musa Zubairu Usman ya zargi gwamnati da rashin tsarin tafiyar da al’amura da hakan ya jefa kasar cikin halin da take ciki.

Shugaba Buhari ya yi umurni ga ma’aikatar kudi ta saki kasafin ga ma’aikatu don fara aiwatar da shi yadda ayyuka za su fara gudana, jama’a kuma su shaida.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:30 0:00

XS
SM
MD
LG