Ba kamar karon farko ba a Qatar a makon da ya gabata, lokacin da tauraron dan kwallon Faransa ya kai ziyara ga abokin wasansa a Paris Saint-Germain a otal din tawagar Morocco da ke cikin garin Doha.
A ranar Laraba mai zuwa, Hakimi zai yi makin din Mbappe a wasan dab da karshe na cin kofin duniya, da zai hana dan wasan Faransa mai buga gaba a gefen hagu ratsa bayan Morocco da suke kare gidansu sosai.
“ACHRAF HAKIMI. Shi ne dan wasan baya da ya fi fice mai buga gefen dama a duniya,” Mbappe ya rubuta a cikin harshen turanci a shafinsa na twitter a watan Janairu, ya na magana game da gurbin dan wasan bayan mai buga gefen dama Hakimi a kulab da kasarsa.
Wannan babban mataki ne ga ‘yan wasan biyu yayin da dukkansu biyu ke fuskantar wasan karshe na cin kofin duniya wanda zai zama tarihi ga kowacce kungiya.
Mbappe da Hakimi, dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar da kwallaye biyar a wasanni biyar a kan gwarzaye da suka yi fice a gasar da aka zura musu kwallo sau daya kacal, kuma dan wasansu ne ya ci gida.
Kyakkyawar abokantakar ta fara ne lokacin da dan wasan Morocco ya koma kungiyar PSG da Mbappe yake a watan Yuli 2021 daga kungiyar Inter Milan kan kudin da ya kai kusan dala miliyan $63M.
Matasan guda biyu an haife su a cikin makonni tsakani a 1998, watannin kadan bayan da Faransa ta lashe Kofin Duniya na farko, nan da nan su ka shaku.
Hakimi ya yi magana game da yadda suke da ra’ayi iri daya a kida da wasannin bidiyo, kuma Mbappe yana taimaka wa abokinsa haifaffan Madri ya koyi harshen Faransanci.