Kungiyar ninkaya zuwa kasan ruwa ta mata ta Scuba tana hada hancin mata a dukan matakan shekaru, da yare har ma da kabila, kan turba daya ta sha’awar shawagi a karkashin ruwa.
Gwamnatin mulkin soji a Burkina Faso ta kori wasu jami'an diflomasiyyar Faransa uku bisa zarginsu da yin zagon kasa, kamar yadda wata takarda da gwamnati ta wallafa a shafukan sada zumunta ta ce ranar Alhamis.
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya yi wa fursunoni sama da 4,000 afuwa, ciki har da wasu da ke jiran hukuncin kisa, a wata afuwar zagayowar ranar bikin ‘yancin kai a ranar Alhamis.
Sojojin Najeriya sun ceto wata mata da ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da ita shekaru goma da suka gabata a lokacin da take yarinya 'yar makaranta a kauyen Chibok, in ji rundunar a ranar Alhamis. An kuma ceto 'ya'yanta uku.
Wani alkalin Najeriya zai yanke hukunci a wata mai zuwa kan ko ya kamata a dawo da belin jagoran 'yan awaren Nnamdi Kanu, a cewar Alkalin kotun ranar Laraba, bayan da a watan jiya kotun ta ki amincewa da sake shigar da kara tare da ba da umarnin fuskantar shari'a cikin gaggawa kan zargin ta'addanci.
Ambaliyar ruwa ta rufe manyan titunan birnin Dubai kuma babban filin jirgin samansa ya kasance cikin rudu yayin da cibiyar hada-hadar kudi ta Gabas ta Tsakiya din ta kasance a kulle a ranar Laraba, kwana guda bayan da aka yi ruwan sama mai tsananin gaske da ba a taba irinsa ba.
Shugaban kasar Mali ya sanar a jiya Talata cewa, kasar Nijar za ta kai lita miliyan 150 na dizal domin samar da wutar lantarki a makwabciyar kasa ta Mali a daidai lokacin da kasar ta yammacin Afirka ke fama da matsalar rashin wutar lantarki.
Hukumomin gundumar Caia sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, kwale-kwalen na dauke da mutane 12 galibi manoma.
Kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta ce ana sa ran wata tawaga za ta isa Togo a cikin wannan mako, yayin da tashe-tashen hankula ke kara ta’azzara game da sake fasalin tsarin mulkin kasar da 'yan adawa suka ce zai tsawaita wa'adin mulkin shugaba Faure Gnassingbe.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International da sauran kungiyoyin kare hakkin bil adama a ranar Litinin sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dakatar da yarjejeniyar da kamfanin Shell ya yi na sayar da wasu kadarorinsa a matsayin wata hanya ta tabbatar da hakkokin al’ummar yankin.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce masu bincike a Najeriya sun kwato kusan dala miliyan 27 a wani binciken cin hanci da rashawa da ya shafi wata ministar gwamnati da aka dakatar da wasu jami'ai.
Hukumar Kwastam ta Senegal ta ce ta kwato fiye da tan guda na hodar ibilis a kudu maso gabashin kasar, inda ta bayyana shi a matsayin kamu mafi girma da aka taba yi na jigilar hodar iblis a kan hanyar kasa a yammacin Afirka.
Iran ta harba jirage marasa matuka masu tarwatsewa tare da harba makamai masu linzami kan Isra'ila da yammacin jiya Asabar - harin da ta kai na farko kai tsaye a kan yankin Isra'ila a matsayin ramuwar gayya da ke kara tsananin barazana a rikicin yankin.
Zaftarewar kasar ta afku ne da tsakar ranar Asabar a gundumar Dibaya Lubwe da ke lardin Kwilu.
Hukumar kula da lafiya ta Afirka ta Kudu ta fada a ranar Asabar cewa za ta janye wani samfurin Johnson & Johnson's (JNJ.N), na sabon maganin tarin yara bayan da aka gano cewa ya na ƙunshe da Diethylene glycol fiye da kima.
Domin Kari