Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da ministar harkokin jin kai da yaki da fatara Betta Edu a watan Janairu sakamakon zarginta da karkatar da kudaden jama’a zuwa asusun banki masu zaman kansu.
Tinubu ya kuma dakatar da shugabar hukumar kula da harkokin zuba jari ta ma’aikatar Halima Shehu bisa zargin almundahana. An kama ta kuma aka sake ta bayan an biya beli, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.
Haka kuma an gayyaci tsohuwar ministar talauci Sadiya Umar-Farouq domin amsa tambayoyi.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Lahadin da ta gabata.
“Bincike ya kuma danganta wasu jami’an ma’aikatar da aka kama da kuma dakatar da su da laifin almundahanar kudi,” in ji ta, ba tare da bayar da cikakken bayani ba.
Tsohon gwamnan jihar Legas, Tinubu ya hau karagar mulki a shekarar da ta gabata inda ya yi alkawarin murkushe masu satar dukiyar kasa a Najeriya, wanda har yanzu kasar na daya daga cikin kasashe na kasa-kasa a jerin masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a ma’aunin Transparency International.
Shugaban na Najeriya ya bullo da sauye-sauyen tattalin arziki tare da dakatar da wasu jami’ai da suka hada da tsohon shugaban babban bankin kasar Godwin Emefiele da tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC a wani bangare na yunkurinsa.
Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka, ta samu karuwar talauci daga kashi 40 cikin 100 na al'ummar kasar a shekarar 2018 zuwa kashi 46 a shekarar 2023, lamarin da ya shafi kusan mutane miliyan 104, a cewar bankin duniya.
Dandalin Mu Tattauna