Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zimbabwe Ta Saki Fursunoni Ciki Har Da Wadanda Aka Yanke wa Hukuncin Kisa


Fursunoni a Zimbabwe
Fursunoni a Zimbabwe

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya yi wa fursunoni sama da 4,000 afuwa, ciki har da wasu da ke jiran hukuncin kisa, a wata afuwar zagayowar ranar bikin ‘yancin kai a ranar Alhamis.

Kasar Zimbabwe ta cika shekaru 44 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka, wanda ya kawo karshe a shekarar 1980 bayan yakin da aka yi da ya hada har da zubar jini. An canza sunan ƙasar daga Rhodesia zuwa Zimbabwe.

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya yi wa fursunoni sama da 4,000 afuwa, ciki har da wasu da ke kan hukuncin kisa, a wata afuwar ranar ‘yancin kai a ranar Alhamis.

Zimbabwean President Emmerson Mnangagwa
Zimbabwean President Emmerson Mnangagwa

Afuwar da shugaban kasar ya yi, wacce ita ce ta biyu cikin kasa da shekara guda, ta amfani fursunoni mata da manya da yara kanana, marasa lafiya da kuma wasu da aka yanke musu hukuncin kisa tun farko.

Wadanda aka taba yanke musu hukuncin kisa amma aka mayar da hukuncin daurin rai-da-rai a cikin umarnin afuwar da suka gabata ko kuma ta hanyar daukaka kara a kotu, za a sake su matukar dai sun shafe akalla shekaru 20 a gidan yari, kamar yadda dokar ta afuwa ta bayyana a ranar Laraba da ta gabata wacce ta fara aiki ranar Alhamis.

Ana ‘yantar da dukkan fursunonin mata da suka yi akalla kashi uku na hukuncin da aka yanke musu ta ranar ‘yancin kai, haka kuma fursunonin matasa da suka yi zaman wannan lokaci.

Fursunonin masu shekaru 60 zuwa sama da suka yi kashi ɗaya cikin goma na hukuncin da aka yanke musu su ma za a sake su. Mnangagwa ya kuma yafewa makafi da nakasassu da suka cika kashi uku na hukuncin daurinsu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG