Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Alkali Zai Yanke Hukunci Kan Belin Shugaban 'Yan Awaren Nnamdi Kanu A Wata Mai Zuwa a Najeriya


Nnamdi Kanu da lauyoyinsa a zaman kotun da aka yi a ranar Alhamis (Channels TV)
Nnamdi Kanu da lauyoyinsa a zaman kotun da aka yi a ranar Alhamis (Channels TV)

Wani alkalin Najeriya zai yanke hukunci a wata mai zuwa kan ko ya kamata a dawo da belin jagoran 'yan awaren Nnamdi Kanu, a cewar Alkalin kotun ranar Laraba, bayan da a watan jiya kotun ta ki amincewa da sake shigar da kara tare da ba da umarnin fuskantar shari'a cikin gaggawa kan zargin ta'addanci.

Kanu, wanda dan kasar Birtaniya ne da ke jagorantar haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), an fara kama shi ne a shekarar 2015 amma ya bace daga Najeriya bayan da aka yi belinsa a shekarar 2017. Daga nan kuma aka kama shi a Kenya a shekarar 2021 kuma aka tuhume shi a Najeriya da laifuka bakwai na ta'addanci. Kanu ya musanta aikata laifin.

Kanu ya musanta saba sharuddan belin na shekarar 2017, yana mai cewa ya tsere ne domin tsira da ransa bayan da sojoji suka mamaye gidan kakansa a jihar Abia da ke kudancin Najeriya. Lauyan da ya shigar da kara ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar Kanu.

Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu

Mai shari’a Binta Murtala Nyako, wadda ta ki amincewa da belin Kanu a watan jiya, ta so a fara shari’ar ne a ranar Laraba.

Nyako ta tsaida ranar 20 ga watan Mayu domin yanke hukunci kan bukatar Kanu na maido masa belinsa ko kuma a kai shi gidan yari ko kuma a daure shi daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

Kungiyar IPOB na fafutukar neman ballewar yankin kudu maso gabashin Najeriya inda akasarin su ‘yan kabilar Igbo ne. Hukumomin Najeriya sun bayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci.

Yunkurin ballewar yankin kudancin kasar a matsayin Jamhuriyar Biafra a shekarar 1967, wato shekarar da aka haifi Kanu, ya haifar da yakin basasa na tsawon shekaru uku, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da miliyan daya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG